Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)

Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)

- Gwmanan jihar Kaduna ya kai ziyara inda aka samu mummunan gobara a garin Tafa

- Malam Nasiru El-Rufai ya jajanta ma mutanen da lamarin ya shafa

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya kai ziyara garin Tafa dake karamar hukumar Kagarko da nufin nuna alhini tare da jajanta ma mutanen da hadarin tankar mai ya rutsa dasu.

Hadarin ya faru ne a ranar Asabar 7 ga watan Oktoba, inda wata motar dakon mai ta kauce hanya, ta afka cikin jama’a, tare da kamawa da wuta, inda nan take ta hallaka mutane da dama.

KU KARANTA: Allah ya yiwa mataimakin shugaban APC a Zamfara rasuwa

A yayin ziyarar tasa, gwamna El-Rufai ya tausaya ma mutanen da hadarin ya rutsa dasu, sa’annan yayi alkawarin tashin tashar manyan motocin daga garin Tafa a yayin daya kai ziyara zuwa sabon filin ajiye manyan motoci da gwamnatinsa ke ginawa.

Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)
El-Rufai

Legit.ng ta ruwaito hadarin ya lakuma sama da gidake 17, tare da babbaka manyan motoci da dama, baya da asarar rayuka da aka yi.

Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)
Inda Gobara ta ci

Kaakakin hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, Yushau Shuaib yace hadarin ya faru ne tsakanin kotar dakon mai da wata karamar mota kirar Golf.

Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)
El-Rufai

Gobara a garin Tafa: El-Rufai ya kai ziyarar gani da ido (Hotuna)
Gobara a garin Tafa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng