An fara binciken wadanda suka balle daga kurkuku a Inugu
- An kulle su ne tsawon shekaru biyu saboda laifin sata
- Sun gude ne a ranar Juma'a da daddare
- An bude sabon layin hura usur
Hukumar kurkukun Najeriya, sashen jihar Inugu ya fara binciken wasu mutane biyu da suke balle daga kurkuku a ranar 6 ga watan Oktoba. Mutanen biyu sune Lucky Sama da Balogun Joseph.
Mai magana da yawun bakin hukumar kurkukun ne, Mista Emeka Monday, ya baiyana wa manema labarai haka.
Yace mutanen sun gudu ne daga kurkukun da misalin karfe 11: 00 na dare a ranar Juma'a. Mista Monday ya ce an kulle su ne na tsawon shekara bibbiyu bisa amsa laifin satar da suka yi a kotun majistre ta Inugu East.
DUBA WANNAN: IPOB ta bayar da umarnin zama a gida domin kauracewa zaben gwamnan jihar Anambara
Ya ce shugaban masu kula da kurkukun, Mista B. N. Ogbodo, ya baza dakaru a cikin jihar don binciko inda wadannan mutane suka buya.
An sa lambar waya ta hura usur in ka san inda wadannan mutane suke: 08063306606.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng