Muhimman bayanai 5 game da Aisha Ahmad, sabuwar mataimakiyar babban bankin Najeriya da Buhari ya nada
A jiya ne dai ranar Alhamis fadar shugaban kasar Najeriya ta ayyana cewa ta tura sunan Aisha Ahmad din zuwa majalisar dattawa don su tantance sannan kuma su tabbatar da ita a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa, CBN a takaice.
Legit.ng dai kamar kullum ta tattaro maku muhimman bayanai guda 5 game da fitacciyar macen da ta fito daga Arewa.
1. An haifi Aishah Ahmad ne a ranar 26 ga watan Octobar shekarar 1976. Yanzu haka tana da shekaru akalla 41 a duniya kuma ta shafe shekaru ashirin tana aikin banki.
KU KARANTA: Ban taba yin boko ba - Dahiru Bauchi
2. Haka ma dai Aisha, 'yar asalin jihar Neja ce dake a arewa ta tsakiyar Najeriya.
3. Ta na da kwarewar aiyyyukan banki sosai don kuwa tayi aiki a wurare da dama irin su bankin Stanbic IBTC da bankin Zenith da kuma bankin New York Mellon. Haka ma ita ta jagoranci sashen harkokin asusun daidaikun mutane a bankin Diamond.
4. Ta yi karatun ta ne a Najeriya da kuma kasar Birtaniya inda tayi digirinta na farko a fannin bayanan da suka shafi kudi watau Akawutin a jami’ar tarayya ta Abuja, sannan ta yi digirinta na biyu a fannin sha’anin kudi a kasar Birtaniya.
5. Haka ma dai mun samu cewa Aisha na auren wani babban tsohon jami'in soji mai suna Birgediya Janar mai ritaya Abdallah Ahmad, kuma Allaha ya albarkace su da 'ya'ya biyu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng