Ban taba koyon karatun Boko ba - Sheikh Dahiru Bauchi
Shahararren Sheihin malamin addinin islamar nan kuma jagoran darikar Tijjaniyya a kasar Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa shi bai taba koyon ko da ABCD ba a makarantar boko.
Shehin malamin yayi wannan karin hasken ne a cikin wata fira da majiyar mu tayi da shi a cikin watan da ya gabata lokacin da ya jagoranci taron addu'oin da ya saba shiryawa a farkon kowace shekarar musulunci.
KU KARANTA: An zargi Ali Modu Sheriff da yin sojan gona
Legit.ng dai ta samu cewa shehin malamin a yanzu haka yana da shekaru akalla 90 a duniya yayin da kuma ya ke da 'ya'ya kimanin 70 kuma dukkan su mahaddata al'qur'ani. Haka ma dai mun samu cewa Shehin malamin ya je hajji sau 48 sannan kuma yaje Umrah sau 200 haka nan kuma ya haddace al'qur'ani mai girma ciki da bai din sa.
Haka ma dai babban malamin da ya fito daga jihar Bauchi ya bayyana cewa yanzu haka yana da mata hudu inda ya ce kuma yanzu haka ya dade da su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng