Yan ta’adda sun hallaka Sojojin Najeriya 5, na Amurka 3 a kasar Nijar
- Yan ta'addan Al-Qaeda sun kai ma Sojojin Amurka da na Najeriya hari
- Rundunar Sojojin Najeriya na da sansani a kasar Nijar
Akalla Sojojin Najeriya biyar da na Amurka uku ne yan ta’adda suka hallaka yayin da suke gudanar da sintiri a kan iyakan kasar Nijar da kasar Mali.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba a wani yankin kasar Nijar da ake tsammanin yan ta’addan kungiyar Al-Qida sun mamaye.
KU KARANTA: Rashin imani: Yadda wani dan fashi yayi ma sa’an Kakansa fashi, kuma ya kashe shi
Kaakakin rundunar Sojojin Amurka dake Najeriya ya tabbatar da faruwar harin, baya da rediyo Faransa suka bada rahoton harin: “Mun tabbatar da labarin kai hari akan hadakan Sojojin Najeriya da na Amurka a kudancin Nijar.” Inji shi
Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jami’in jakadancin Najeriya yace yan ta’addan sun shigo ne daga kasar Mali, kuma yace sun kashe Sojoji da dama. Tuni an sanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump dangane da harin, ta bakin shugaban ma’aiatan fadar White House, John Kelly.
A wani labarin kuma, Rediyo Faransa ta zakulo wani labara dake nuna cewa Sojoji zasu mayar da biki a wani shiri na yin gangamin Sojojin hadin gwiwa tare da manyan makamai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng