Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki

Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki

- Akonda mai shekaru 32 ya yi wa diyar matar sa ciki a Legas

- Mai laifin ya fada ma alkali a kotu cewa son diyar matar sa yake yi

- Akonda yayi alkwarin daukar nauyin angolan sa da yayi wa ciki

Jami’an yansandar jihar Legas sun kama wani mutum mai suna Saka Akonda da yi wa agolan sa mai shekaru 13 ciki.

Yansada sun kama Akonda mai shekaru 36 bayan dan uwan mahaifin yarinyar ya kai karar sa wajen hukuma.

Akonda wanda ya gurfana a gaban kotu majistri dake Ogba, ya fada ma alkali cewa yana son yarinyar ne.

Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki
Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki

Mai laifin yayi mamaki da yansada suka kama shi bayan yayi sulhu da ainihin mahaifin yarinyar.

KU KARANTA : Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

Mai laifin wanda ya kasance yana da yara biyu, yayi alkwarin daukar nauyin agolan sa da ya yi wa ciki.

Yac e, “tsakanin shi da mahaifin yarinyar babu wata matsala, dan uwan mahaifin yarinyar ke kawo mu su matsala.

“Shi ya ingiza mahaifin yarinyar ya sa a kama ni. Ko lokacin da matata ta ce mu zubar da cikin na ki amince wa.

“Ina tsoro ka da ta mutu. Ni ke daukar nauyin karatu ta tun lokacin da matata ta kawo ta gida na.

“Kuma mahaifinta ya yaba da irin dawainiyyar da nake yi ma diyyar sa.”

Akonda ya ce “dansandan da yakama shi ya bukaci naira N50,000 a wajen sa dan sassanta matsala da mahaifin yarinyar, amma dubu goma kadai ya iya ba dawa.

Ya kara de cewa: “Yana son mahaifin ya tuna yadda yake kula mishi da diyar sa, wanda ya yi watsi da ita.

Akonda yace “matar sa ta barshi bayan yansanda sun kama shi.

Kawun yarinyar, Oladele Rasheed, yace mahaifiyar yarinyar ta rabu da dan uwansa shekaru biyar da suka gabata, ta je ta auri mutumin banza.

“Mutumin da ya yiwa uwa da diyyar tac ciki.

“Ko da dan uwana ba zai yi komai ba game da wannan al’amari, sai na tabbatar da an hukunta shi akan wannan mumunar aika-aika da yayi

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng