Ga Dalilin da zai sa ku kalli wadannan sababbin fina-finan hausa guda 5
Duk farkon shekara ake sakin sababbin fina-finai domin nishadantar tare da fadakar da masu kallo. Amma a wasu lokutan masu shirya fina-finai kan sake sakin wasu fina-finan a tsakiya ko kuma karshen shekara.
Ga wasu jerin fina-finai guda 5 da marubuta da furdososhi da jarumai suka taka rawar burgewa cikin shirin.
1. Rariya: Fitacciyar 'yar wasa Rahama Sadau ta dauki nauyin shirin.
2. Kalan Dangi: Shirin babban darekta Ali Gumzak, kuma shahararriyar 'yar wasa Aisha Aliyu Tsamiya ta dauki nauyin shirin
3. Mansoor: Ali Nuhu ne ya bayar da umarnin shirin, sannan Umar M. Shariff da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahaya suka fito a jarumai.
DUBA WANNAN: Babbar matsalar masana'antar shirya fina-finai ta kannywood - Farfesa Abdallah Uba Adamu
4. Rumana: Shirin kamfanin Hikima multimedia mai dauke da fiattun jarumai kamar su; Rahama Sadau, Adam Zango, da Aminu Shariff Momo.
5. Kujerar Wuta: Shirin na dauke da gogaggiyar tsohuwar tauraruwa, Hauwa Maina, wacce ake wa kirari da "mai idon zinare".
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.co
Asali: Legit.ng