Garabasa! Farashin buhun shinkafa kilo 50 zai koma Naira 15,000 nan ba da dadewa ba - Minista
Babban ministan gona a Gwamnatin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta Cif Audu Ogbe yayi wa yan Najeriya bushara da cewa buhun shinkafa yar gida mai nauyin Kilo 50 zai dawo kan Naira 15,000 nan ba da dadewa ba.
A yanzu dai binciken mu ya tabbatar mana da cewa ana saida buhun shinkafar mai kwatankwacin wannan nauyin a kan Naira dubu 17 zuwa dubu 18 a kasuwanni.
KU KARANTA: Darajar Naira ta kara farfadowa
Legit.ng ta samu dai cewa ministan yayi wannan busharar ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja babban birnin tarayya.
Ministan wanda dan asalin jihar Benue ne ya labarta cewa yanzu haka suna nan tattaunawar su tayi nisa da masu sarrafa shinkafar inda tuni suka bayyana masu babbar matsalar da ke ci musu tuwo a kwarya sannan kuma suka fara zayyana hanyoyin maganci matsalolin da nufin kawo sa'ida ga talakawan Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng