Atafau sai an aura min wanda nake so: Yarinyar Ganduje ta lashi takobin auren Bayarabe

Atafau sai an aura min wanda nake so: Yarinyar Ganduje ta lashi takobin auren Bayarabe

Soyayya gamon jini ce amma inda kauna, inji wani mawakin Hausa, tarihi ya nuna halin da wasu masoya kan shiga da zarar an nemi a hana musu abinda zuciyarsu ke kauna, da dama kan shiga mawuyacin hali.

Wannan shine kwatankwacin takaddamar dake tasowa a gidan gwamnatin jihar Kano, inda diyar gwamnan jihar, gwamna Abdullahi Ganduje ta lashi takobin sai ta auri sahibinta bayarabe, inji rahoton Daily Nigerian.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bani muhimmiyar shawara dangane da zaɓen 2019 – Inji Nasir El-Rufai

Diyar gwamnan mai suna Fatima Ganduje ta tsaya kai da fata, atabau lallai sai ta auri saurayinta bayareba, mai suna Idris Abiola Ajimobi, wanda da yake ga gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Atafau sai an aura min wanda nake so: Yarinyar Ganduje ta lashi takobin auren Bayarabe
Gwmana Ajimobi, Idris da Fatima

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito hakan bai yi ma iyayen Fatima dadi ba, inda suka dauki dukkanin matakin da suke ganin zai kawo karshen soyayyar Fatima da Idris ta hanyar kwace wayoyinta, kamar yadda wani makusancin su ya shaida ma majiyar mu.

Duk haka, Fatima, bata daina so tare da kaunar Idris ba, inda a ranar 19 ga watan Satumba ta dauta hotonsa a shafinta na Instagram (Fateeganduje), don ta bayyana ma duniya karara cewa tana nan akan bakanta.

Fatima diyace ga gwamnan jihar Kano, daya daga cikin yayan gwamna Abdullahi Ganduje, kuma ta kammala karatunta na digiri daga jami’ar ABTI dake Yola, yayin da shi kuma saurayin nata Idris, da ne ga gwamnan jihar Oyo, kuma shima Musulmi ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng