Manoma 200,000 suka amfana daga biliyan 44 a shirin gwamnatin tarayya – Inji Buhari
- Shugaba Buhari ya ce akalla manoma 200,000 suka amfana daga naira biliyan 43.9 na shirin gwamnatin tarayya
- Shugaban ya ce manoma sun samu tallafin kudi ta hanyar CBN da wasu hukumomi 13
- Shugaban kasa ya ce dole ne a ci gaba da daidaita arzikin kasar don kada a dogara ga man fetur kadai
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akalla manoma 200,000 a fadin kasar suka amfana daga naira biliyan 43.9 na shirin gwamnatin tarayya a kan bunkasa harakar noma.
An fara shirin ne tun watan Nuwambar 2015.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaban kasa, wanda ya sanar da wannan a cikin sakon tuna da ranar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktober a Abuja, ya ce aikin aiwatar da wannan shirin ya kasance "kyakkyawar nasara".
A cewar shugaban, an sako adadin wannan tallafin ga manoma ta hanyar babban bankin Najeriya (CBN) da kuma hukumomi 13.
KU KARANTA: 2019: Buhari ya je ya huta ya bar zance kara tsayawa takara - Akinjide
Ya bayyana cewa shirin ya ƙunshi kadada 233,000 na gona.
Shugaba Buhari ya ce tare da yawan ruwan sama a bara da wannan shekara, aikin noma a kasar ta samu taimakon Allah.
Shugaban ya ci gaba da cewa dole ne gwamnati ta ci gaba da daidaita arzikin kasar don kada a dogara ga man fetur kadai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng