Shin ko kun san wa ya kera tutar Najeriya? Mai kore da fari? Kuma meye ma'anar kalolin?

Shin ko kun san wa ya kera tutar Najeriya? Mai kore da fari? Kuma meye ma'anar kalolin?

- A bikin cikar Najeriya shekaru 57 da kafuwa a matsayin gamammiyar tarayyar kasa, wadda aka faro tun 1914, sai gashi an samo wanda ya hado tutar kasar nan da ransa

- Hira da Aljazeera ta bashi damar fadin yadda yayi tunanin tutar, launin ta da ma'anar ta

- Har yanzu yana raye, kuma kai baka ce ya sami wata muhimmiyar dukiya ya tara ba

Michael Taiwo Akinkunmi yana karatu injiniya ne a 'Norwood Technical College London' dake kasar Ingila a shekarar 1959, kuma yana da shekarun haihuwa 23 lokacin da ya shiga gasar kirkirar tutar Najeriya kuma daga bisani yayi nasara har ya samu kyautar kudi fan 100 (Dala 281) a shekarar 1959 da kuma samun matsuguni cikin kundin tarihin Najeriya.

Shin ko kun san wa ya kera tutar Najeriya? Mai kore da fari? Kuma meye ma'anar kalolin?
Shin ko kun san wa ya kera tutar Najeriya? Mai kore da fari? Kuma meye ma'anar kalolin?

Mista Akinkunmi na rayuwa ne yanzu a matsayin dan fansho a garin Ibadan a gidansa dake cikin unguwar talakawa inda ko hanyar mota babu. Akinkunmi yace tafiya mai tsawo da yayi tun bayan da ya bar aiki, ita ce zuwa Abuja a shekarar 2014 lokacin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya karrama Shi tare da kirkirar masa albashin dundundun na naira dubu 800, Wanda yace duk wata ana biyan shi har yanzu.

Akinkunmi yanzu haka na fama da matsalar mantuwa domin yace bazai iya tuna mai tsohon shugaban kasa Jonathan ya fada masa ba lokacin da ya gayyace shi, hakazalika ya kasa tuna sunayen abokansa na kuruciya, hasali ma dai bai iya fadin sunan makarantar da yayi a Ingila daidai ba, sannan ya kasa tuna dalilin da yasa akayi masa tiyata jim kadan bayan ya bar aiki a shekarar 1993.

DUBA WANNAN: Ashe tiriliyoyi ake turawa jihohi, suka yi mukus basu sanwa talakka

Akinkunmi yanzu haka nada shekara 79 na haihuwa kuma fentin gidansa kore da fari ne kamar yadda yayi fentin tutar Najeriya. Ya ce kalar tutar na nufin noman mu, arzikinmu, mutuncin mu, da kimar mu a idon duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng