Kasar Kamaru za ta datse iyakar ta da Najeriya
Legit.ng ta na samun rahoton cewa, gwamnatin kasar Kamaru ta zartar da dokar ta baci a yankunan Kudu maso Yammacin Kasar mai amfani da harshen turanci sabanin harshen kasar na Faransanci, sakamakon zanga-zanga da al'ummar yankin suka shirya na neman ballewa daga kasar a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.
A wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta kaddamar da dokar takaita zirga-zirga tun daga yammaci zuwa safiya tare da datse iyakar ta da kasar Najeriya saboda masu ballewar.
Shugaban kasar na Kamaru Paul Biya tare da yarjejeniyar gwamnan yankin Kudu maso Yammacin kasar, ya shirya matakai inda ya bayar da umarni ga rundunar sojin kasar akan su tashi tsaye wajen wanzuwar zaman lafiya tare da bayar da tsaro ga 'yan kasar na gari.
KARANTA KUMA: Najeriya ta kara sama zuwa mataki na 125 a jerin kasashen masu habaka ta fuskar tattalin arziki
A makon da ya gabata, shugaban kasar ya fitar da wata sabuwar doka da take ta fayyace ka'idar takaita zirga-zirga a yankim Kudu Maso Yammacin kasar, wadda ya ce za ta fara aiki daga ranar 29 ga watan Satumba zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.
Wannan zanga-zanga da al'ummar yankin Kudu maso Yammacin kasar za su gudanar ta zo ne, sakamakon tunawa da ranar samun 'yan cin kai na ranar 1 ga watan Oktoba a shekarar 1961.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng