Gwamnatin Saliyo ta kama wani faston Najeriya don yin maganganu masu ban tsoro game da Islama
- Jami’an tsaro a kasar Saliyo sun kama wani faston Najeriya mazaunar kasar don yin maganganun da bai dace ba a kan musulumai
- An kama faston ne bayan rikodin maganansa a kan musulumai ya yadu a shafukan yanar gizo
- Shugaban sashen bincike na laifuka na Saliyo ya ce, sakon faston ya ba kowa haushi a kasar
Wani faston Najeriya mazaunar kasar Saliyo, Victor Ajisafe ya shiga hannun jami'an tsaron kasar bayan da aka same shi da laifin yin maganganu masu ban tsoro game da addinin Islama a lokacin ibada na ranar Lahadi.
An kama faston ne bayan rikodin maganansa a kan musulumai ya yadu a shafukan yanar gizo a kasar.
Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ruwaito cewa Ajisafe, wanda shi ne shugaba kuma wanda ya kafa cocin “The Sanctuary Praise Church” daya daga cikin cocin da yafi girma a kasar.
Yayin da yake magana da mabiya addininsa ya zargi addinin Musulunci a matsayin addinin tashin hankali da ƙarya da kuma yaudara, ya kara da cewa Musulmai suna da alhakin duk wani ta'addanci a tarihin duniya.
KU KARANTA: Rikici ya sa za a toshe bakin iyakar Najeriya ta Kasar Kamaru
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, kasar Saliyo na da kusan 78% na musulmi, bisa ga wani bincike ta shekarar 2015 wanda cibiyar bincike ta Pew Research Center estimate ta gudanar.
An kama fasto a ranar Talata da ta gabata, amma ba'a caje shi ba har yanzu.
Shugaban sashen bincike na laifuka na Saliyo, MB Kamara, ya ce, "Sakonsa ya ba kowa haushi”.
“Mu masu addini ne kuma babu wanda ya damu da cewa wani musulmi ko krista. Dukanmu muna zama da juna cikin lafiya har tsawon zamani, kuma babu wanda yake so wannan dagantakar ta baci", inji shi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng