Mutu ka raba, takalmin kaza: Mutuwa kaɗai zata raba ni da kujerar Sanata – inji Bukar Abba
Tsohon gwamnan jihar Yobe, kuma Sanatan al’ummar yankin Yobe ta gabas, Sanata Bukar Abba Ibrahim yace ba zai taba dai na tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa ba har iya rayuwarsa.
Sanata Bukar Abba ya bayyana haka a bainar majalisar dattawa, yayin da ake tafka muhawara akan bikin cikar Najeriya shekara 57 da kafuwa, inda yace mutuwa ce kadai zata raba shi da kujerar Sanata.
KU KARANTA: An fitar da sunayen sabbin Malamai 178 da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauka
Sanata Bukar na majalisar dattawan ne a karo na uku, inda ya dare kujerar tun a shekarar 2007, bayan daya kammala wa’adin mulkinsa a jihar Yobe, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka Bukar shine shugaban kwamitin kulawa da sauyin yanayi a majalisar dattawa, yayin da matarsa kuma tsohuwar yar majalisar wakilai, daga nan kuma ta zama ministan Najeriya.
Sai dai ana tunanin Sanatan ya aika da sakon ne ga gwamnan jihar Ibrahim Geidam, wanda zai kammala wa’adinsa na gwamnan jihar Yobe a shekarar 2019, kuma ya fito daga mazaba daya da gwamnan jihar, wanda ake gani shima na sunsunan kujerar.
“Mun gode ma Ubangiji Allah da yan Najeriya, ina bayyana ma shugaban majalisar dattawa ce ba zan bar majalisar dattawa ba iya rayuwana, har sai na mutu, saboda jama’a na ma haka suke kira na.” Inji Sanata.
Da yake mayar da martani, Sanata Bukola Saraki cikin raha yayi kira ga Sanata Ahmad Lawan da Sanata Mohammad Hassan wadanda dukkansu yan jihar Yobe ne da su kula da maganan da Sanata Bukar Abba yayi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng