A raba aurenmu, mijina baya bani abinci – Wata mata ta bayyanawa kotu
Wata matar auren Hafsat Mohammed, ta bukaci wata kotun Shari’a da ke zaune a Minna ta raba aurenta da mijinta saboda baya cepane a gida.
Hafsat ta bayyanawa kotu cewa mijinta, Isah Gimba, yana banner kudinsa kan shaye-shaye ne a maimakon kula da gida.
“Maigidana bai samar da abinci a gida, dan kudin da yake samu shaye-shaye yakeyi da shi. Bakar wahalar da nike sha a gidan ya isheni haka.”
“Shi yasa nike rokon wannan kotu ta raba wannan auren na huta.”
KU KARANTA: Najeriya tayi hobbasa a bangaren tattalin arziki
Amma mijinta, Gimba, ya musanta wannan zargi da matarsa ke masa kuma ya jaddada cewa shi fa yana son matarsa har yanzu.
An dakatar da karan zuwa ranan 9 ga watan Oktoba domin yin sulhu tsakaninsu.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng