Kasar Saudiyya ta dakatar da yada karatun babban malamin salafiyyar kasar
Kasar Saudiyya ta dakatar da yada duk wani karatu na babban Malamin Salafiyyar nan na Kasar Fauzan Bin Fauzan.
Sakamakon fatawar da ya bada akan ranar bikin kafuwar kasar da ya gudana a makom nan inda aka cakudu maza da mata ana murnanr wannan ranar zagayowar kafa kasar da suke kira da abun da ba'a taba samun irin shi ba tun kafuwar kasar.
KU KARANTA: Majalisar wakillan Najeriya ta shiga cikin rikicin Ganduje da Kwankwaso
Legit.ng dai ta samu cewa wannan dalilin yasa Babban Malamin yace wannan abu da akayi Bidi'a ne hakan yasa Hukumar kasar duk da irin mutuncin da yake dashi Suka dakatar da yada duk wani karatun Shi har illa Masha'Allah.
Idan dai mai karatu ba zai manta ba kasar ta Saudiyya tayi wani gagarumin taro domin tunawa da ranar ta game ta zama kasa guda daya tilo.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng