Sahihin jagoranci: Wani babban malamin darika ya yi babban abun koyi a Kano
Wani babban shehin malamin darika a Najeriya daga jihar Kano mai suna Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara ya shiga cikin leburori tare da daukar bahon siminti a kansa yayin da ya ziyarci inda ake gina wani masallaci.
Masallacin da aka yi wa lakabi da masallacin marigayi Malam Buhari yana a unguwar Mandawari ne a cikin kokuwar garin na Kano.
KU KARANTA: Yan shi'a sun gamu da babban cikas a Arewa
Legit.ng ta samu dai cewa manyan mutane irin sa masu tarin dubban mabiya basu cika yin irin wannan halin na tawali'u ba musamman ma dai yadda ake kallon kamar aikin kaskanci ne.
Wannan kyakkyawan halin da ya nuna har ila yau ya zuwa yanzu yana ta samun yabo da kuma addu'oi daga jama'a da dama.
Wani daga cikin mutane mai suna Halipha Yahya Tal Udu cewa yayi: "Wannan abu yayi kyau ya kamata sauran malamai suyi koyi da wannan tsarin domin karfafa gwiwar mabiyan su wajen aikin alheri Allah yasa mudace."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng