Kamfanin Sadarwa na Airtel, ya kaddamar da aikin gudummawarsa ta fannin ilimi a Kaduna
- Kamfanin sadarwa na Airtel ya yi bikin bude firamaren Yahaya Hamza dake Zaria
- Gwamnan jihar Kaduna ya godewa kamfanin sadarwar na Airtel bisa kokarin su na tallafawa bangaren ilimi a fadin Najeriya
- Manajan kamfanin Airtel a Najeriya ya bayyana cewar sun zabi tallafawa bangaren ilimi ne saboda muhimmancin ilimin a rayuwa
Kamfanin sadarwa na Airtel ya yi bikin bude, firamaren Yahaya Hamza dake Zaria, daya daga cikin makarantun da suka dauki nauyn tallafawa da kayan koyarwa domin inganta ilimin yara marasa galihu.
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa'i, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron, godewa kamfanin sadarwar na Airtel bisa kokarin su na tallafawa bangaren ilimi a fadin Najeriya. Gwamnan ya kara da cewa, makarantar firamare yanzu ta samu karin jerin dakuna 6 masu dauke da ajuzuwan koyarwa 12, bencina, kujeru, ofishin malamai, allon bango, da kuma bandakunan malamai dana dalibai maza da mata. Gwamnan ya rufe jawabin sa da kira ga ragowar kamfanunuwa da suyi koyi da aikin kirki irin na Airtel.
DUBA WANNAN: Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben shekarar
A yayin jawabin sa, babban manajan kamfanin Airtel a Najeriya, Segun Ogunsanya, ya bayyana cewar sun zabi tallafawa bangaren ilimi ne saboda muhimmancin ilimin a rayuwa.
Makarantar firamare ta Yahaya Bello dake Zaria ita ce makaranta ta biyar da kamfanin na Airtel ya zaba domin tallafawa. Ragowar sune; Oremeji firamare a jihar Lagos, firamaren St. John's dake Ogun, firamaren Amumara dake Imo, firamaren Iyeru Okin a Kwara, da firamaren Presbyterian a jihar Kuros Riba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng