Duk da hadarin dake ciki, zubar da ciki na faruwa sau miliyan 56 duk shekara - Hukumar kula da lafiya ta duniya

Duk da hadarin dake ciki, zubar da ciki na faruwa sau miliyan 56 duk shekara - Hukumar kula da lafiya ta duniya

- Hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayyana cewar duk shekara ana zubar da ciki kusan sau miliyan 56

- Wani bincike ya nuna cewar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014 an zubar da ciki sau miliyan 55.7 duk shekara

- Mafi yawan hadarin dake faruwa yayin zubar da cikin na faruwa ne a nahiyar Afrika

Wata jaridar kasar Birtaniya mai suna "Guardian" ta buga wani rahoton bincike na hukumar kula da lafiya ta duniya da ya bayyana cewar duk shekara ana zubar da ciki kusan sau miliyan 56 duk kuwa da hadarin dake cikin hakan, kuma mafi yawan hadarin dake faruwa yayin zubar da cikin, na faruwa ne a nahiyar Afrika.

Duk da hadarin dake ciki, zubar da ciki na faruwa sau miliyan 56 duk shekara - Hukumar kula da lafiya ta duniya
Duk da hadarin dake ciki, zubar da ciki na faruwa sau miliyan 56 duk shekara

Wani bincike ya nuna cewar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014 an zubar da ciki sau miliyan 55.7 a kowacce shekara, kamar yadda yazo a cikin wata mujallar lafiya mai suna Lancet.

DUBA WANNAN: Kamfanin jirgin sama na "British Airways" zai yi jigilar 'yan Najeriya kyauta don nuna murnar zagayowar ranar samun 'yanci

Bincike ya nuna cewar miliyan 17.1 na zubar da cikin na zuwa da hadari domin masu son zubar da ciki basa bin ka'ida ki hanyar data dace domin zubar da ciki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng