Amurka ba ta yarda da cewa IPOB 'yan ta'dda bane — Lai Mohammed
- Najeriya ta maida IPOB kungiyar 'yan ta'adda saboda batakashin da aka yi tsakanin su da sojojin Najeriya
- An tattauna da Lai Mohammed a BBC a kan cewa to ya ke nan America ita kuma bata yadda ba?
- Biyafara ta kaddamar da gwamnatin ta, kudin ta, fasfo, da kuma sojojin ta
Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya baiyana cewa Amurka bata yadda cewa kungiyar IPOB kungiyar 'yan ta'adda bane. Ya fadi haka ne a tattaunawar da aka yi da shi a gidan labaran BBC, labaran Afirka, a ranar Laraba.
"Maganganun da Nnamdi Kanu da 'yan IPOB suke yi maganganu ne na ta'addanci. Akwai kasikan da aka dauka na Kanu yana cewa suna son su kwaci Biyafara ta karfin tsiya, kuma in ba'a basu ba sai Somaliya ta zamo aljanna ga abin da Najeriya zata shiga."
Da BBC ta tambayi Lai Mohammed cewa ya za'a yi mutumin da bai dau makami ba a ce ya zama dan ta'adda? Lai ya ce, "Shine dai mutumin da ake tara makamai da yawun sa, kuma ya hada sojojin sa kuma har sun yi fada da sojojin Najeriya."
An tambayi Lai Mohammed to yaya ke nan tun da Amurka ba ta yadda da cewa 'yan tadda bane?
"Abin bai yi dadi ba. Bai kamata a ce ko wacce kasa da wadanda zata yadda cewa 'yan ta'adda ne da kuma wadanda bata yarda ba. Kamata yayi a hada karfi gaba daya don a karar da ta'addanci a doron kasa."
An kuma tambaye shi cewa to me yasa makiyayan da suke ta kashe-kashe a jihohin Najeriya ba'a ce 'yan ta'adda bane?
DUBA WANNAN: Sojojin kamaru na cin zarafin 'yan gudun hijirar Najeriya dake kasar
Ya ce, "Kashe-kashe kadai ba shi yake zama da kungiya 'yan ta'adda ba. IPOB ta maida kan ta 'yan ta'adda saboda ta hada gwamnatin ta a cikin Najeriya, ta yi kudin ta, ta yi fasfo dinta, kuma tana bi kasashe-kasashe tana rokon makamai."
Daga karshe BBC ta tambaye shi ba'a tsoron wannan batu da aka yi ya kara nausa IPOB a cikin abin da suke yi har tarzomar tafi ta da?
"Najeriya lange-lange ce. Za muyi iya kokarin mu a ce abin bai kai ga haka ba."
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng