Duk nisan jifa, ƙasa zata faɗo: An bankaɗo wani sansanin Sojojin gona a jihar Benuwe
Rundunar Sojin ruwa ta yi ma wasu Sojojin gona diran mikiya yayin da suke gudanar da atisaye a garin Opokgu dake jihar Benuwe, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.
Wadannan Sojin bogi masu suna ‘Costal Defence Force, 4th Arms Signal Ship Base operating’, wato Sojojin ruwa na musamman, kamar yadda suka bayyana kansu, suna zambatar samari ne da nufin shigar dasu aikin Soji.
KU KARANTA: Rikici akan shanu ya sanya wani Bahillace ya datse kan abokinsa
Sai dai jami’an Sojin ruwan Najeriya sun samu rahoton ayyukan matasan, inda suka kai samame a sansanin su, suka kuma samu sa’ar kama katta 24 da shekarunsu bai gaza 24 ba.
Yayin samamen, Sojojin sun kama matasan ne sanye cikin Khakin Soja, sa’annan suna dauke da bindigu, yayin da sauran ke dauke da adduna da wukake.
Bugu da kari Sojojin Najeriya sun gano wasu manyan hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da na gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom da kuma hotunan wasu manyan Sojojin bogin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng