Hukumar sojin sama ta kasar Jordan zata hada gwiwa da takwararta ta Najeriya domin yaki da ta'addanci
- Hukumar sojin sama ta kasar Jordan zata hada gwiwa da takwararta ta Najeriya domin yaki da ta'addanci
- Kwamandan sojin saman na kasar Jordan ya bayyana cewar hadin gwiwa domin yakar ta'addanci shine abinda duniya ke yayi yanzu
- Sojin Najeriya ta dau alwashin samar da zaman lafiya a kasa
Hukumar sojin sama ta kasar Jordan Royal Jordanian Air Force (RJAF), ta bayyana niyyarta na hada gwiwa da sojin sama na Najeriya domin fatattakar ta'addanci da ayyukan 'yan tayar da kayar baya.
Kwamandan sojin sama na kasar Jordan, manjo janar Yousef Alhanaity, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kaiwa babban hafsan sojin sama na Najeriya, Abubakar Sadique, a sansanin sojin sama na Najeriya dake Abuja. Kwamandan sojin saman na kasar Jordan ya bayyana cewar hadin gwiwa domin yakar ta'addanci shine abinda duniya ke yayi yanzu.
Kwamandan da suke tare da rundunar RJAF ya shaida yadda yakin sama shine wanda zai kawo karshen ta’addanci, hukumar zata samarwa da hukumar sojin Najeriya horo da tallafi wajen yaki da ta’addanci.
Babban hafsun sojan Abubakar Sadiq ya ce ba kasar da zata iya yaki da ta’addanci ita kadai face da taimakon wasu kasashen. Ziyarar da Hukumar sojin ta kasa tayi a kwanan-nan zuwa kasashen Amirka, Ingila, Rasha, Pakistan, Saudiyya da kasar Jordan sun yi don kulla babbar alaka tsakanin kasashe .
DUBA WANNAN: Dubi jerin kasashe 9 masu makamin kisan kare dangi na nukiliya
Sojin saman Najeriya ta dau alwashin hadin kai da RJAF. Tuni hukumar sojin RJAF ta bawa sojin najeriya uku horo a kasar Jordan sannan za a cigaba da bawa wasu horo a kan yaki da ta’addanci.
Manjo janar Yusuf Alhnairty da tawagar sa zasu kai ziyara sansanin soji a Maiduguri da Yola wanda zai gana da matukan jirgin sama. Hukumar sojin zata dau duk wani mataki don cika umarnin su na tsarin mulki na tsare zaman lafiya na kasa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng