An kammala shirye-shiryen dawowar Buhari Najeriya daga asibitin Landan
Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar Najeriya gida ranar Litinin bayan kammala abin da ya kai shi London.
Shugaban ya tafi London ne ranar Alhamis bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka.
Daya daga cikin jami'an da suka raka shugaban Amurka ya tabbatarwar da majiyar mu cewa cewa tsarin tafiye-tafiyen mai gidan nasa ya nuna cewa zai koma kasar ne ranar ta Lahadi kamar dai yadda BBC ta ruwaito.
KU KARANTA: Yan sanda sun saki dan jaridar NAN da suka kama
Legit.ng dai ta samu cewa kafin tafiyar tasa London, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Da ma dai fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya.
A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng