Ku bamu sassan jikin matattu domin inganta lafiyar rayayyu, inji wani likitan zuciya a Najeriya
- Likitan zuciya ya roki 'yan Najeriya da su dinga bada sadakar sassan jikin 'yan uwansu masu anfani bayan sun mutu domin taimakawa marasa lafiya mabukata
- Addini, al'adda da camfi na taka muhimmiyar rawa wajen kin amincewar 'yan Najeriya
- Gwamnati ya kamata ta wayar wa da mutane kai a kan taimako ga marasa lafiya
Dakta Kola Olawale wani likitan zuciya ya roka ga ‘yan Najeriya da su dinga bada sadakar sassan jikin mamatan su ga marasa lafiya mabukata.
Dakta Kola yace 'yin hakan ba wani sabon abu bane a kasashen da suka ci gaba domin sun dauki yin hakan ma tamkar girmamawa ga mamacin da kuma maras lafiya da aka sadaukarwa da sassan jikin amma abin takaici a Najeriya bama yin hakan saboda dalilai na al'ada da addini.'
Likitan yace 'na sha jin mutane a Najeriya na cewa ba zasu iya sadaukar da wani bangare na jikinsu ba saboda zasu koma ga ALLAH ne a yadda ya halicce su. Amma asalin abin da ke faruwa shine idan mutum ya mutu aka binne shi a cikin kasa, jikin shi bayan shekaru yana rubewa, a maimakon a yi asarar sassa masu anfani zai dace ace an bawa mabukata kyauta domin ceto ran su.'
A cewar likitan ‘ na dade ina aikin asibiti wanda sau da yawa marasa lafiya zasu zo neman lafiya amma su ga cewa sai an musu aiki an canja musu zuciya wanda sai dai su hakura.'
Ya kara da cewa ‘ Ya fi muni a Najeriya domin kuwa bamu da kayan aiki kwararru sannan kuma saboda wasu dalilai na addini da al’adu wasu mutanen suke ganin yin hakan a matsayin babban laifi’. Canfi ma na taka muhimmiyar rawa wajen kin amincewar 'yan Najeriya, a saboda haka ya kamata gwamnati ta shigo domin wayar da kan jama'a a kan muhimmancin hakan'.
Wani likita Kenneth Azubuike, ya yadda da dalilan likitan da kira ga gwamnatin tarayya da ta sanarwa da mutane anfanin sadakar da sassa na jikin ga mabukata.
Wata Joyce Effiom, likitar mata ta shaidawa NAN yadda ta ji dadi bayan ta bada sadakar zuciya da kodar marigayin dan ta ga mabukata. Lokacin da yana shekara biyar ya yi hatsarin mota. Bayan mutuwarsa ta ji labarin wata yarinya a asibitin tana fama da ciwon koda, da aka gwada sai aka yi dace, haka aka sawa yarinyar kodar, zuciyar sa ma daga baya aka samu wanda ta dace da shi. Yin hakan ba karamin farin ciki ya sa uwar yaron ba.
DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa wasu ma'aikatan NGO shekara 9 gidan yari
'Ko a baya ansha fama da 'yan Najeriya kafin su yarda su fara bayar da jini, haka ma yanzu na san za a dauki lokaci kafin 'yan Najeriya su fahimci muhimmancin sadaukar da sassan jikin mamaci.
A shekaru 10 da suka wuce, mutane na dari-darin bada kyautar jini a asibiti, amma da gwamnati ta yada sanarwa da wayarwa da mutane kai sai aka samu sauki, yanzu mutane sun gane bada jini ga mabukata sadaka ne da taimako.
Likitan ya kira da gwamnati ta bi hanyar da ta bi na wayar wa da jama'a kai na bayar da jini a samu mutane su dinga bada sadakar sassa irin su zuciya ko koda ga mabukata.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng