Jalingo: kungiyar Mutum Biyu ta tallafa wa marayu 120 a Taraba

Jalingo: kungiyar Mutum Biyu ta tallafa wa marayu 120 a Taraba

- Kungiyar ci gaba ta Mutum Biyu a karamar hukumar Gassol na jihar Taraba, ta shigar da marayu 120 a makarantun firamare a jihar

- Shugaban kungiyar ya ce shirin na daga cikin kokarin da kungiyar ke yi don inganta rayuwar marayu a jihar

- Shugaban ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da ba da fifiko ga ilimi don samun daidaito tare da sauran al'ummomin da suka ci gaba a fanin ilimi

Kungiyar ci gaba ta Mutum Biyu (MBDA) a yankin karamar hukumar Gassol na jihar Taraba, ta shigar da marayu 120 a makarantun firamare a jihar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Tukura Julde, wanda ya bayyana hakan a wani jawabi da manema labarai a Jalingo a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, ya ce yana daga cikin kokarin da kungiyar ke yi don inganta rayuwar marayu a jihar.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Julde ya ce kungiyar ta biya wa marayu kudin makaranta kuma ta samar masu da tufafi da kayan karatu da takalma da sauran bukatun kuma za ta dauki nauyin bukatun marayun har zuwa aji na shida.

Jalingo: kungiyar Mutum Biyu ta tallafa wa marayu 120 a Taraba
Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar tallafa wa marayu saboda akwai yawancin yara wadanda ba su da wanda zai kula da ilimin su da sauran bukatunsu.

KU KARANTA: Aisha Buhari zata tallafawa mata 1000 a Bauchi

Alhaji Tukura ya bayyana cewa abin takaici ne idan aka lura da cewa 'ya'ya da yawa da suka rasa iyayensu a yankin ba za su iya zuwa makaranta ba saboda rashin masu tallafawa.

Ya kuma kara da cewa ƙungiyar ta kuma ba da tallafin kudi ga dalibai 120 wadanda ke manyan makarantu a dukan faɗin ƙasar.

A cewar shugaban, ƙungiyar za ta ci gaba da ba da fifiko ga ilimi don samun daidaito tare da sauran al'ummomin da suka ci gaba a fanin ilimi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng