Iran ta shiga sahun Korea ta Arewa wajen gwajin makami mai linzami

Iran ta shiga sahun Korea ta Arewa wajen gwajin makami mai linzami

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa kamar dai yadda kasar Koriya ta Arewa ta yi, kasar Iran ta kammala gwajin sabon makamin ta mai linzami a ranar Jumma'ar da ta gabata a filin faretin dakarun sojin ta dake babban birnin Tehran.

Wannan makami mai linzami da kasar ta Iran ta bayar da sunan sa na 'Khorramshahr' zai iya yin tafiya mai nisan mil 1250 wato dai kilomita 2000, wanda rahotannin suka bayyana cewa da wannan nisan tafiyar zai iya isa kasar Isra'ila da Saudiya.

Iran ta shiga sahun Korea ta Arewa wajen gwajin Nukiliyya mai kare dangi
Iran ta shiga sahun Korea ta Arewa wajen gwajin Nukiliyya mai kare dangi

A jawabin ranar Jumma'ar da ta gabata na shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya bayyana cewa kasar za ta cigaba da inganta harkokin tsaronta, kama daga kara karfin nukiliya da kuma karfin dakarun soji, wanda hakan zai sa kasashe suyi shakkun takalarta da kuma rashin neman taimakon wata kasar wajen ba ta kariya.

KARANTA KUMA: Duniya ta lalace: A shekarar 1974 Najeriya ta baiwa 'IMF' rancen kudi

Ya kara da cewa, "ko ana so ko ba a so sai mun taimakawa kasashen Syria, Yemen da kuma Falastin, kuma za mu karfafa nukiliyyoyin mu".

Rouhani ya ce kasar Amurka da Isra'ila sun ware kan su ta hanyar nuna rashin goyon bayan yarjejeniyar Nukiliyya da aka kulla a shekarar 2015, tsakanin kasar ta Iran da sauran kasashe masu karfin Nukiliyya. Ya ce har yanzu kasar ta Iran ta na nan akan wannan yarjejeniya.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng