Za a dauka sabbin jami’an ‘yan sanda 31,000 a Najeriya
- Sufeto Janar na 'yan sandan (IGP) ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake dauka karin 'yan sanda 31,000
- Hukumar ‘yan sanda ta yaye wasu jami’an ‘yan sanda 854 daga Kwalejin 'yan sanda da ke Oji River a jihar Enugu
- IGP ya bukaci ‘yan sanda su kasance masu girmama wa 'yancin ɗan adam yayin gudanar da aikin su
Sufeto Janar na 'yan sandan (IGP), Ibrahim Idris, a ranar Juma'a, 22 ga watan Satumba ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, don amincewa da daukar da kuma horar da jami’an ‘yan sanda 10,000 a shekarar 2016.
Duk da haka, Idris ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake dauka karin 'yan sanda 31,000 a cikin shekaru biyar masu zuwa, don cimma tsarin na dan ‘yan sanda guda ɗaya ga kimanin mutane 400 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci.
Ya bayyana haka yayin da yake jawabi a bikin yaye wasu jami’an ‘yan sanda 854 daga Kwalejin 'yan sanda da ke Oji River a jihar Enugu.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Idris wanda mataimakin Sufeto na ‘yan sanda (DIG) wanda ke kula da bincike da tsare-tsare, Mista Valentine Ntomchukwu ya wakilta.
KU KARANTA: Buratai ya bayyana sirrin da yayi anfani da shi wajen farfado da karsashin sojin Najeriya
IGP ya bukaci jami’an su aiwatar da ayyukansu a cikakkiyar biyayya ga bin doka, yayin da kuma ya ce su tabbatar cewa sun girmama wa 'yancin ɗan adam na kowane mutum yayin gudanar da aikin su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng