Likita ya fitar da wani abun mamaki a cikin tumbin wani
Wani likita an ruwaito wai cewar ya fitar da kayan mata dan kamfai da rigar mama a cikin tumbin wani mutum a kasar Amurka.
A kwanan baya ne dai labarin yadu a kasar ta Amurka inda aka ce wai likitan ya fitar da abun al'ajabin.
Legit.ng dai ta samu cewa labarin dai ya fita ne sakamakon sanya hotunan kayan sawar na mata da likitan yayi a shafin sa na sada zumunta na Instagram sannan kuma ya bayyana yadda lamarin ya faru.
A wani labarin kuma, Rahotanni daga Fadar Shugaban kasa sun nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Muhammad Buhari zai yi waje Rod da wasu ministoci goma a cikin sabuwar shekara bisa rashin tabuka komai tun bayan da aka rantsar da su.
Wata majiya da Fadar Shugaban ta nuna cewa za a kuma yi wa wasu ministocin canji ma'aikatu wanda ya dace da kwarewar su. An dai jima ana hasashen Buhari zai dauki wannan mataki musamman yadda ake ci gaba da koke a kan wasu ministocin nasa wadanda suka shige ribibi.
To fa! Ko me yakai wannan a cikin dan adam?
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng