Zamu cigaba da kera makaman Nukiliya saboda diyan banza - Kasar Iran

Zamu cigaba da kera makaman Nukiliya saboda diyan banza - Kasar Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce Tehran ba ta da bukatar izinin ko wacce kasa a duniya kafin ta kera makaman kare-dangi.

Da yake jawabi a yayin faretin sojoji a Tehran, Shugaba Rouhani ya ce Iran ba za ta daina karfafa dakarun sojinta ba.

Ya kuma ce za a kara karfin dakarun sojin kasar domin nuna bijirewa.

Zamu cigaba da kera makaman Nukiliya saboda diyan banza - Kasar Iran
Zamu cigaba da kera makaman Nukiliya saboda diyan banza - Kasar Iran

KU KARANTA: Inyamurai a Adamawa sun watsawa IPOB kasa a ido

Legit.ng ta samu cewa dai a jawabinsa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Trump ya zargi Iran da kera makaman kare-dangi masu hatsari, kuma ya bayyana yarjejeniyar da ta kulla da kasashe masu karfin fada-a-ji a matsayin abin kunya.

A yayin faretin, dakarun tsaro na Iran sun gabatar da makaman kare-danginsu masu nisan matsakaicin zango wanda ake kira "Khoramshahr", wanda suka ce yana iya kai wa nisan kilomita 2,000 kuma zai iya daukar makamai da yawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng