A kawo dauki! Ni Musulmi ne amma ina ganin na fara rasa imanina zuwa Arne – Dan Najeriya
Legit.ng ta ci karo da rubutu da wani mutum ya yada kan damuwarsa bisa barin hanyar addinin musulunci da jingina kan kafurci.
A cewar rubutun, mutumin mai suna Abdulkabir, yace yaji tsoro cewan imanin shi ga addinin musulunci yana raguwa.
Ko da yake ya cigaba da daukaka ayyukan addinin musulunci, yace ya tsinci kanshi cikin matukar yarda da aminci a fannin kimiya bisa yarda da koyarwar addinin Islama.
Ya kuma daura wa shedan cewa “shedan yana rudar da shi” yana kuma kokarin maishe shi kafiri.
Yayinda yake bayyanawa a rubutun sa, ya rubuta cewa; aminci shi tabbata gare ku yan uwana maza da mata a addinin Islam. Bari in fada muku kai tsaye.
Ina bukatan taimakonku da jagorancinku saboda imanina yana raguwa a koda yaushe, na fi ganin gaskiya al’amura cikin fasaha fiye da addini.
KU KARANTA KUMA: Babu wanda zai taba Hausawan dake zaune a kudancin kasar nan – Ohaneaze
Wasu lokuta sai in dunga ji kamar ina bata lokacina ne bisa addini, ban san ko shedan bane yake kokarin rudar dani, amman kullun ina tunani marasa amfani.
Bayanin kula: ina da bangare mai kyau da kuma marasa kyau.
Bangare mai kyau; "Bana tsallake sallolina biyar a rana, kuma ina salloli 3-4 cikin 5 a jam’i, da wuya ace ban samu jam’in juma’a ba, bana “zina”, ina bayar da sadaka ga mabukaci, bana shan giya balle ganye.
Bangare marasa kyau; "Bana karanta Al-qur’ani a ko da yaushe, tun bayan watan Ramadana da wuya in taba Kur’ani, bana azumi sai dai na watan Ramadana, zuwa gidan rawa ya kasance halina yanzu, da wuya in sallaci sallar subhi a jam’i.
"Amman matsalar ita ce, duk lokacin da nayi sallah sai inji bana da imani, da wuya inji kamar ina mu’amala da Ubangijina, ku taimaka, imani yana sauka a ko da yaushe.
"Mahaifina ya yi karantu a boko mai zurfi har baya kulawa da abunda ya shafi addini, mahaifiyana kuma ta kasance daga gida mai riko ga addini a kauyenta.
"Ina ganin na gaji mahaifina ne, ina neman taimako, ina ji ne kamar ina komawa ga kafirci.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng