Kano: Gobarar wuta ta halaka mutane 4 a Kano
- Gobarar wuta ta halaka mutane 4 a birnin Kano
- Wutar ta rushe dukkanin dakuna hudu a cikin gidan da gobarar ta shafa
- Daraktan hukumar kwantar da gobarar wuta ya danganta gobarar akan ajiyar man fetur a cikin gida
Akalla mutane hudu sun mutu sakamakon wani mumunar gobarar wuta a safiyar ranar Laraba, 20 ga watan Satumba a Tudun Murtala Quarters a cikin birnin Kano.
Babban daraktan hukumar kwantar da gobarar wuta na jihar, Alhaji Mustapha Rilwan, ya shaida wa majiyar Legit.ng a Kano a ranar Alhamis cewa, wutar ta rushe dukkanin dakuna hudu a cikin gidan da gobarar ta shafa.
A cewarsa, "Wani dan taliki ya kira mu a ranar Laraba misali karfe 10:23 na safe cewa ana gobarar wuta a wani gida a Tudun Murtala Quarters. Yayin samu wannan labari nan da nan muka tura motocin kashe wuta 4 zuwa gidan inda muka yi nasara kashe wutar bayan mintuna 45”.
Rilwan ya ce sun samu ceto mutane 4 yayin da mutum daya ya ji rauni kuma an kai shi asibitin Murtala Mohammed na musamman.
KU KARANTA: Gwamnatin Kwara ta bawa nakasassu masu wasan kwallon kwando kyautar kujerar guragu
Ya ce likita ya tabbatar da cewa mutane 4 daga cikinsu sun mutu yayin da mutum daya da ya saura ana masa magani a asibitin.
Daraktan ya danganta gobarar wutar akan ajiyar man fetur a cikin gida kuma ya shawarci mazauna su kaucewa adana kayan man fetur a gidajensu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng