Sauki ya zo: Kayan masarufi sun fadi wanwar a jihar Gombe (Hotuna)
Mazauna jihar Gombe sun dara da yiwa Ubangijinsu godiya sanadiyar yadda kayan masarufi suka yi sauki musamman ma shinkafa wadda mafi yawan al'ummomin yankunan Arewa suka fi amfani da ita.
Shafin jaridar Rariya na yanar gizo ya ruwaito yadda al'ummar jihar suke murna da kuma godiya ga Ubangijnsu kan yadda aka samu saukin kayan abinci a jihar.
KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta datse yunkurin Diezani na barin kasar Birtaniya
A can baya jama'a da yawa musamman ma na yankunan Arewa a kasar nan, sun yi kukan tsadar rayuwa musamman abinci ta hanyar kukan yunwa, wanda da yawansu ke alakanta abin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, sai kuma gashi yanzu sauki ya zo.
Wani mazaunin jihar ya zayyana a shafin dandalin sada zumunta cewa, "Alhamdulillah sauki dai Allah ya kawo mana shi wannan karon ma, kamar yadda shinkafa ta yi tashin gwauron zabi a baya, sai ga shi yau mun wayi gari ta sauko akan farashin 250 da 230 kowane mudu".
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng