Gargadin Amurka Na Ruguza Koriya Ta Arewa: Koriya Ta Kudu Ta Goyi Bayan Shugaba Donald Trump Na Amurka

Gargadin Amurka Na Ruguza Koriya Ta Arewa: Koriya Ta Kudu Ta Goyi Bayan Shugaba Donald Trump Na Amurka

- Shugaba Donald Trump ya shaidawa taron Majalisar Dinkin Duniya cewa Amurka zata rusa Koriya ta Arewa idan har tura ta kai bango

-Shugaban kasar Koriya ta kudu, Moon Jae-in, ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Donald Trump

- Kasar China ta bayyana cewar za a iya shawo kan wannan matsala ne ta hanyar siyasa da diflomasiyya kawai

A wani jawabi daya fito daga ofishin shugaban kasar Koriya ta kudu, Moon Jae-in a yau laraba, kasar Koriya ta kudun ta bayyana goyon bayanta ga jawabin da shugaba Donald Trump yayi a jiya yayin gudanar da taron majalisar dinkin duniya, na cewar zai ruguza kasar Koriya ta Arewa.

Gargadin Amurka Na Ruguza Koriya Ta Arewa: Koriya Ta Kudu Ta Goyi Bayan Shugaba Donald Trump Na Amurka
Koriya Ta Kudu Ta Goyi Bayan Shugaba Donald Trump Na Amurka

"Mun aminta cewar akwai bukatar zaman lafiya a duniya, don haka bayanin shugaba Donald Trump akan dai-dai yake kuma muna goyon bayansa domin ya nuna cewar kasar Amurka ba zata kawar da kai wasu tsirarun kasashe su zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba".

Ya kara da cewa "Mun yabawa kokarin shugaba Trump na ganin kasar Koriya ta Arewa ta lalata tare da daina kera makamin nukiliya kuma kamar yadda yayi kira ga shugabannin duniya musamman kasashen China da Rasha dasu matsawa kasar ta Koriya ta Arewa ta amsa kiran da yayi mata, muma muna kara kira domin kara matsin lamba ga Koriya ta Arewa har sai tayi biyayya ga kiran na shugaban Amurka"

DUBA WANNAN: Duniya Makwantar Rikici: Shugaban Amurka Donald Trump Ya Shaidawa Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Cewa Amurka Za Ta Wargaza Koriya Ta Arewa

Kasar China, wacce duniya ke ganin itace ke marawa Koriya ta Arewa baya, ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje, Lu Kang, ta bayyana cewar za a iya shawo kan wannan matsala ne ta hanyar siyasa da diflomasiyya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng