Duniya tayi zafi: Wani tsoho mai shekaru 70 ya yi kundunbala a cikin rijiya

Duniya tayi zafi: Wani tsoho mai shekaru 70 ya yi kundunbala a cikin rijiya

Wani tsoho mai shekaru 70 a duniya dake garin Otukpo a jihar Benue, ya bar mazauna unguwarsu ta Okokoro cikin jimami da abin al'ajabi, yayin da ya jefa kan sa cikin wata tsohuwar rijiya.

Shafin Daily Post ta bayar da sunan wannan tsoho a matsayin Inuwa kadai, yayin da aka tsinto gawarsa a wata tsohuwar rijiya dake yankinsu, kuma ya kashe kan sa ne ba tare da barin wata rubutacciyar wasiya ba akan dalilin da ya sanya shi aikata wannan mummuna aiki.

Mazauna wannan yankin sun bayyanawa manema labarai cewa, tun a ranar Juma'ar da ta gabata suka nemi Inuwa suka rasa, domin a tunaninsu ko ya yi batan hanya ne bayan wata fita da yayi.

Tsohuwar rijiyar da Inuwa ya jefa kan sa
Tsohuwar rijiyar da Inuwa ya jefa kan sa

Gogan naku ashe ya na cikin wata tsohuwar rijiya dake yankin na su, yayin da wayewar garin na ranar Asabar din da ta gabata, mazauna yankin suka ga motsin gawar sa a cikin rijiyar yayin diban ruwa kamar yadda suka saba.

KARANTA KUMA: Labari cikin Hotuna: Aisha Buhari ta sanya rigar Dalar Amurka 4490 a wajen tarbar shugaban kasar Uganda da uwar gidansa

Mallam Inuwa ya mutu ya bar 'ya'ya bakwai, kuma a halin yanzu an sanya gawar a makwancinta a can mahaifarsa ta unguwar Odogomu dake karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng