Kotu ta daure wani tela watanni 5 bisa laifin cin amana da karya alkawari

Kotu ta daure wani tela watanni 5 bisa laifin cin amana da karya alkawari

Wata kotun tarayyar Najeriya mai matsayi na daya a unguwar Kado dake a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yankewa wani tela mai suna Iliyasu Isah kukuncin daurin watanni 5 a gidan yari sakamakon samun sa da tayi da laifin cin amana da kuma karya alkawari.

Haka ma kuma dai alkalin kutun a cikin hukuncin nasa ya ba Telan zabin biyan tarar Naira dubu 6 sannan kuma da biyan kwastoman nashi diyyar Naira dubu 25.

Kotu ta daure wani tela watanni 5 bisa laifin cin amana da karya alkawari
Kotu ta daure wani tela watanni 5 bisa laifin cin amana da karya alkawari

KU KARANTA: Na kusa dawowa harkar fim - Zainab Indomie

Legit.ng haka ma kuma ta samu cewa Alkalin kotun daga nan ne sai ya shawarci telan da ya canza hali ya bar cin amana kuma ya zama mai cika alkawari a cin sana'ar sa.

Tun farko dai dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun cewa wani kwastoman telan ne mai suna Malam Isa ya kai wa telan dinkin sa amma sai kawai telan ya saida kayan akan kudi Naira dubu 25 sannan kuma yayi ta yi masa yawo da hankali.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng