Asara goma-da-goma! Sabon tsadajjen dan wasan Barcelona ya tafi jinyar watanni 4
Sabaon shahararren dan wasan nan na kungiyar barcelona dake a kasar Spain da aka siya akan makudan kudaden da suka kai dalar Amurka miliyan 125 mai suna Ousmane Dembele ya samu rauri a wasan sa na farko da kungiyar.
Haka ma kuma dai kamar yadda muka samu shine cewa raunin da ya samu za'ayi masa tiyata be a a kasar Finland kuma zai iya shafe kimanin watanni hudu kafin ya gama murmurewa.
KU KARANTA: Real Madrid ta farfado bayan doguwar suma
Legit.ng dai ta samu daga kungiyar ta dan wasan ta Barcelona cewar sun bayyana a wata sanarwar su da cewa: "Dan wasan mu Dembele yanzu haka ya kama hanyar zuwa kasar Finland inda za'ayi masa aiki kan raunin da ya samu a kafar sa ta hagu."
A wani labarin kuma dai kungiyar kwallon kafar nan ta Real Madrid dake a kasar Spain ta farfado daga doguwar sumar da tayi bayan da ta shafe wasanni biyu a jere tayi yin kunnen doki da nasarar da ta samu akan kungiyar Real Sociedad.
A wasan dai wani matashin dan gaban nan ne dai ya samu nasarar zura kwallon sa ta farko a babban wasa mai suna Borja Mayoral yayin da kuma ya hadda kwallon ta biyu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng