IPOB: Rundunar sojan Najeriya ta kara yawan sojoji don hana nau’i hare-hare a Zaria

IPOB: Rundunar sojan Najeriya ta kara yawan sojoji don hana nau’i hare-hare a Zaria

- Rundunar sojin Najeriya ta kara yawan sojoji masu sintiri a titin garin Zaria da kewaye

- Birgadiya Janar Victor Ezegwu ya shawarci jama'a kada su ji tsoro domin yawan sojoji masu sintiri a titin garin Zaria da kewaye

- Kwamandan ya ce sojoji na shirye kowane lokaci don tallafawa al’umma ta hanyar da ta dace

Rundunar sojin Najeriya ta kara yawan sojoji a matsayin matakan da zai hana duk wani nau'i na hare-hare a Zaria, bayan rahotanni na hare-haren da kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara, IPOB suka kai wa ‘yan arewa mazauna a yankin kudu maso gabashin kasar.

Wannan ta ƙunshe a cikin wata sanarwa daga mataimakin daraktan hulda da jama’a na makarantar horar da sojan Najeriya (MNS), Capt. Haruna Mohammed-Sani.

Ya bayyana cewa kwamandan makarantar horar da sojan Najeriya, Birgadiya Janar Victor Ezegwu, ya sadu da jami’an tsaro ciki har sojoji da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an aiwatar da matakai masu dacewa.

IPOB: Rundunar sojan Najeriya ta kara yawan sojoji don hana nau’i hare-hare a Zaria
Dakarun sojin Najeriya

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, kwamandan ya shawarci jama'a kada su ji tsoro domin yawan sojoji masu sintiri a titin garin Zaria da kewaye.

KU KARANTA: Hukumar sojin saman Najeriya NAF ta yaye dalibai 150

"Rundunar sojin Najeriya ta kasance a shirye kowane lokaci don tallafawa al’umma ta hanyar da ta dace a duk lokacin da aka bukace ta don kare rayuka da dukiya", inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng