Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba

Kwallon kafa ta zama hantsi leka gidan kowa domin duk lungu da sako na duniya babu inda ba zaka iske ana kallo ko tattaunawa a kanta ba. Duk da kasancewar wasu sun dauki taurarin wasan kwallon kafa a matsayin ababen koyi, hakan ba yana nuna taurarin basu da kashi a gindinsu ba.

Wadannan taurarin 'yan wasan kwallo kafa guda 5 sun taba aikata laifin kisan kai a rayuwar su:

1. Marcos Alonso: Dan wasan kungiyar Chelsea dake Ingila. Ya taba kashe wata mata mai shekara 19 a Madrid dake Spain a yayin da yake tsula gudu a mota ana ruwan sama. Anyi masa hukuncin daurin shekara 4 a gidan yari kafin daga bisani a sake shi bayan diyyar yuro 500,000 ga iyalan matar.

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba
Marcos Alonso

2. Patrick Kluivert: Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake Spain, Kluivert, ya taba kashe wani shahararren mai shirya wasan kwaikwayo a kasarsu ta Neitherland, bayan ya rambatsi motar mai shirya wasan kwaikwayon da motar abokinsa kirar BMW M3.

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba
Patrick Kluivert

3. Bruno Fernandez de Souza: A shekarar 2010, an gurfanar da tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Flamingo dake Brazil, Fernandez, da laifin azabtarwa tare da kisan budurwarsa. A watan fabrairu na shekarar nan ya fito daga kurkuru amma kotun daukaka kara a kasar ta Brazil ta sake maida shi kurkuru domin karasa zaman hukuncin daurin shekara 22 da akayi masa tun a farko.

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba
Bruno Fernandez de Souza

DUBA WANNAN: Fafutikar 'Yan Awaren Biafra Ta Rasa Kima Tun Bayan Da Suka Fara Tayar Da Hankulan Jama'a - Gwamnonin Yankin Kudu Maso Gabas

4. Diego Buonanotte: Abokin wasan Lionel Messi a kasar Argentina kuma tare suka ciyowa kasar Argentina lambar zinare a wasan olamfik ta shekarar 2008. A shekarar 2009, Buonannote, da wasu abokansa uku sukayi hadari a hanyarsu ta dawowa gida daga casu. Duk ragowar abokan uku sun mutu amma Duononnotte ya tsira da ransa kuma bayan warkewarsa wata kotu a kasar ta Argentina tayi umarni a tsare shi bisa zarginsa da aikata kisan kai.

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba
Diego Buonanotte

5. Alexandre Villaplane: Dan asalin kasar Algeria, haihuwar Faransa, Villaplane, ya jagoranci kasar Faransa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 1930. Ana tuna Villaplain ne da muguwar rawar daya taka a kisan sama da mutum 50 a Mussidan. A shekarar 1944 kotu tayi masa hukuncin kisa ta hanyar harbi a bainar jama'a.

Bincike: Fitattun 'Yan Wasan Kwallon Kafa 5 Da Baku Taba Sanin Sun Aikata Laifin Kisan Kai Ba
Alexandre Villaplane

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng