Rikicin Biyafara: Yan arewa dake zaune a kudu sun bukaci Shugaba Buhari ya kara tura dakarun sa a yankin

Rikicin Biyafara: Yan arewa dake zaune a kudu sun bukaci Shugaba Buhari ya kara tura dakarun sa a yankin

Wasu ayan arewacin Nageriya dake zaune a kudu masoo gabashin Nigeria sun roki gwamnatin tarayyan kasar data taimaka ta kara yawan yawan jami'an tsaro a yankin na kudu maso gabas.

Haka ma dai yan asalin arewacin Nigeriyar dake zaune a yanikin na kudu maso gabashin kasar sun yaba da kokarin gwamnatin tarayyanar na dakile tarzomar data kunno kai a yankin.

Legit.ng ta dai samu cewa amma sai dai sun kuma yi kira ga gwamnatin ta tarayya data kara adadin jami’an tsaro a yankin.

Rikicin Biyafara: Yan arewa dake zaune a kudu sun bukaci Shugaba Buhari ya kara tura dakarun sa a yankin
Rikicin Biyafara: Yan arewa dake zaune a kudu sun bukaci Shugaba Buhari ya kara tura dakarun sa a yankin

KU KARANTA: Bancin naman alade ko shan giya - inji matar da tafi kowa shekaru

Suka ce duk da yake lamura sun lafa amma har yanzu suna cikin halin fargaba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa rundunar sojin kasar ta kaddamar da wani shirin samar da tsaro a yankin da suka yi wa lakani da 'rawar mesa' sakamakon tarzomar da kungiyar nan dake fafutukar kafa kasar Biafara ta ke neman tadawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng