Farashin kayan abinci ya sauka a Asaba

Farashin kayan abinci ya sauka a Asaba

- Bincike ya nuna farashin kayan abinci ya fara sauka a Asaba

- Masu siyan kaya a kasuwa sun nuna farinciki akan yadda farashin abinci ya sauka

- Manoma sun ce iseshen ruwan sama da aka yi a wannan shekara ya sa inganta amfanin noma

Binciken da yan jaridan News Agency of Nigeria (NAN) suka yi a kasuwan Asaba ya nuna farashin kayan abinci Kaman garri, doya dankalin turawa ya fara sauka.

Masu siyan kaya a kasuwan Ogbe Ogongo a ranar Lahadi, sun nuna farinciki akan kokarin da dilolin kayan abinci suka yi wajen tabbatar da farashin abinci ya sauka.

Wasu manoma sun ce an samu karin amfanin noma a wannan shekara ta dalilin isashen ruwan sama da aka yi wanda yayi sanadiyar saukar farashin kayan abinci.

Farashin kayan abinci ya sauka a Asaba
Farashin kayan abinci ya sauka a Asaba

Wata dilan kayan abinci Angela Okonta ta fada ma yan jarida cewa a da ana sayar da buhun garri N20,000 amma yanzu ya koma N17,000.

KU KARANTA : Biyafara : Abun da Buhari ya shirya yi wa kabilan Ibo – Fani Kayode

Tace a watan Yuni an sayar da karamin bukitin gari N,1000 amma yanzu ya ana sayar N700.

A watanni biyu da suka gabata an sayar da jakar dankalin turawa N2,000 amma yanzu farashin ya koma N1,400.

Ana sayar da madaidacin doya N500 ko N600 amma yanzu ya koma N300 ko N400 ya danganta da yadda mai saye yayi ciniki.

Wani mai sayar da shinkafa Eugene Nkechor ya fada wa yan jarida cewa a da ana sayar da buhun shinkafa N18,000 amma yanzu ya koma N17,000.

Da muna sayar da karamin bukitin shinkafa N2,000 ama yanzu ya koma N1.600.

Yace farashin farin wake ya sauka kadan daga N16,500 zuwa N15,000.

Nkechor yace da ana sayar da karamin bukitin wake N1,500 amma yanzu ya koma N1,500.

Wani manomi mai suna Obi yace doyan dake yawo a kasuwa yanzu wanda aka shuka ne a karshen shekarar da ta gabata tsakanin watan Nawumba da Disamba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng