Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)

Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)

- Al’ummar Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji

- Wata yar jarida ta wallafa wasu hotuna a yanar gizo wanda ke nuna al’ummar Hausawa a bakin kasuwancin su

- Hotunan nuna mutane sun fara koma bakin aikin su ba tare da wata takura ba

A cewar rahotanni da aka tattara daga Aba a jihar Abiya, halin da ake ciki yanzu zaman lafiya ta fara dawo cikin yankin bayan tashin hankali tsakanin mambobi na kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara IPOB da jami’an tsaro na rundunar sojin kasar na wasu kwanaki.

Legit.ng ta tattaro cewa, wata yar jarida mai suna Linda Osuala wanda ta zagaya garin Aba ta wallafa hotuna wanda ta ke nuna halin da Hausawa da ke zaune a garin ke cikin a yanzu.

Hotunan nuna cewa mutane sun fara koma bakin aikin su na yau da kullum ba tare da wata takura ba.

Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)
Al'ummar Hausawa a Aba

KU KARANTA: Kabilar Igbo mazauna Kano sunce basu tare da Nnamdi Kanu

Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)
Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su

Idan dai ba a manta ba, a farkon makon nan ne sojojin Najeriya suka mamaye garin Aba, al’amarin da jawo wata rikici tsakanin sojoji da ‘yan kungiyar IPOB.

Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)
Zaman lafiya ta sake dawo garin Aba

Aba: Hausawa mazaunar Aba sun koma bakin kasuwancin su bayan arangama tsakanin IPOB da sojoji (Hotuna)
Ayyuka sun sake dawo kamar yadda aka saba a Aba

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng