An samu hatsaniya a Gwagwalada a tsakanin wasu kungiyoyin adawa 2

An samu hatsaniya a Gwagwalada a tsakanin wasu kungiyoyin adawa 2

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani rahoto da ba’a tabbatar ba me cewa wata sabuwar cikici ta balle a garin Gwagwalada dake babban birnin tarayya Abuja sakamakon kisan wani mutum a ranar Juma’a 15 ga watan Satumba.

Rkicin ya barke ne tsakanin wasu kungiyoyi masu adawa da juna a cibiyar kasuwancin garin Gwagwalada, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Dubun wani ɗan fashi daya shahara wajen kashe mutanen da yayi garkuwa dasu ya cika (Hotuna)

Wani mazaunin yankin, wanda ke sana’ar Kanikanci yace duk masu shagunan yankin sun kukkule, sun kama gabansu don gudun abin da kaje ka dawo.

Sai dai wasu rahotannin sun shaida cewar tuni Sojoji suka bazama, kuma sun kwantar da tarzoman da ta taso sakamakon hatsaniyar data kaure a garin.

Wata mata mai shago a garin, tace Sojoji sun umarce ta data kulle shagonta ta koma gida, “Sun bani umarni da na wuce gida kai tsaye ba tare na tsaya a wani wuri ba.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng