Abin Al-ajabi: Kalli wata hallita da aka gani a gabar tekun Amurka
Jama’a sun shiga cikin fargaba yayin da aka suka ci karo da wata mummunar dabba da ba’a taba ganinta ko a tarihi ba a jihar Texas na kasar Amurka, inji rahoton BBC Hausa.
An hangi wannan dabba ne bayan da wata guguwa mai karfi da iska da aka yi ma lakabi da Harvey ne ta sharo wannan dabbar daga cikin Teku zuwa gabar tekun da aka tsince shi.
KU KARANTA: Tsanin kishi ya sanya wata mata ta jefa 'ya'ya mata 2 na kishiyarta cikin rijiya
An samu hoton halittar ne daga shafin wata mata ma’abociyar kafar sadarwar zamani na Twitter mai suna Preeti Desai inda ta ke neman karin bayani daga masana ilimin dabbobi.
“Masana Ilimin halittu, menene wannan kuma?” kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito. Sai dai wani masanin ilimin dabbobin ruwa, Dokta Kennith Tighhe, wanda yace dabbar tafi kusa da siffar maciji, sai dai tana da hakora. Hakazalika Kennith yace halittar ka iya zama wani nau’i na kifi mai kama da maciji
Ita ma matar data gano wannan dabbar, ta shaida ma BBC cewa “Ba’a taba ganin irin wannan dabbar ba, wannan ba dabbar da aka saba gani bane a cikin teku ba, amma ina ganin daga tsakiyar teku ta fito.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng