Kananan yara 2 da wasu mutum 7 sun jikkata a wani hatsarin mota a Abaji

Kananan yara 2 da wasu mutum 7 sun jikkata a wani hatsarin mota a Abaji

Kimanin mutane 9 ne suka samu raunuka sanadiyyar wata mummunan hatsari data auku a tsakanin motar Bas akan hanyar Abuja zuwa Lokja, kamar yadda Dily Trust ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar ALhamis 14 ga watan Satumba, yayin da direban wata Sienna ya rasa kan motar tasa, inda ya afka ma motar Bas din.

KU KARANTA: Yadda wata Amarya ta wurga ýaýan uwargidarta cikin rijiya

Hakan ya sanya direban motar taka birki,wanda yayi sanadiyyar fashewar tayar motar, inda nan da nan mota ta fara wuntsulawa har sai da fada cikin daji, yayin da ta zubar da fasinjojinta.

Kananan yara 2 da wasu mutum 7 sun jikkata a wani hatsarin mota a Abaji
Hatsarin mota

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ba tare da bata lokaci bay an FRSC suka iso inda hatsarin ya auku, inda suka garzaya da mutanen zuwa asibiti. Shima shugaban FRSC na yankin Olasupo Esuruoso ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda yace sun kai wadanda suka jikkata asibitin garin Abaji.

Olasupo ya danganta hatsarin da gangancin direba da kuma fashewar taya, sa’annan yayi kira da direbobi da su dinga bin ka’aidojin tuki don su tsiratar da rayuwarsu dana fasinjojinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng