Hanyoyi 7 da Ronaldo ya bambanta da sauran yan wasan kwallo

Hanyoyi 7 da Ronaldo ya bambanta da sauran yan wasan kwallo

Tun dai ba yau ba a koyaushe muhawara ta kan yi zafi musamman a tsakanin masu sha'awar kwallon kafa akan shin wai takamai-mai wanene dan wasan da yafi shahara a duniyar kwallo.

Masana da dama kan tada jijiyoyin wuya wani lokacin ma kuma hadda kumfan baki musamman a wannan zamanin kuma idan aka kawo batun yan wasan nan biyu shahararru watau Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo.

Legit.ng dai ta samu cewar Shi dai Cristiano Ronaldo ya fito ne daga kasar Portugal inda kuma yanzu haka yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake a kasar Spain.

Abubuwan da ya bambanta Ronaldo da sauran 'yan wasa su ne:

1. Shi kadai ne ya ci kwallo 107 a gasar cin kofin zakarun Turai

2. Zai iya buga tamaula da komai, ba sai da kwallo ba.

3. Ya ci kwallon zakarun turai da yawa fiye da Man United tun shekarar 2009/2010, inda ya ci kwallo 92 Man United kuma 89

Hanyoyi 7 da Ronaldo ya bambanta da sauran yan wasan kwallo
Hanyoyi 7 da Ronaldo ya bambanta da sauran yan wasan kwallo

KU KARANTA: Yadda wasu yan kasuwa ke saye abinci suna boyewa

4. Ronaldo ya bude gidan tarihi da ya sadaukar wa kansa

5. Ba wanda yake buga tamaula da kai kamar Ronaldo

6. Mutum ne mai baiwa

7. Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai hudu.

Abin tambayar anan shi ne, ko Ronaldo zai lashe kofi na biyar a bana?

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng