Akalla 'yan kasuwa 53 ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a Kebbi

Akalla 'yan kasuwa 53 ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a Kebbi

- Fiye da ‘yan kasuwa 53 suka mutu sakamakon wani mummunar hadarin jirgin ruwa a garin Bagudo da ke jihar Kebbi

- Mafi yawan 'yan kasuwar suna daga kauyen Gaya a Jamhuriyar Nijar

- Shugaban karamar hukumar Bagudo ya ce daga cikin fasinjoji 100 da ke cikin jirgi, mutane 47 kawai aka ceto

Shugaban karamar hukumar Bagudo da ke jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Zagga, ya tabbatar a yau Alhamis, 14 ga watan Satumba cewa fiye da mutane 53 ‘yan kasuwa suka mutu a cikin wani hadarin jirgin ruwa a kogin Neja a garin Bagudo da ke.

Zagga ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a wata hira a wayar tarho cewa mutanen suna zuwa kasuwa ne lokacin da lamarin ya faru.

“Mafi yawan 'yan kasuwar sun kasance daga kauyen Gaya a Jamhuriyar Nijar”.

"Suna zuwa cin kasuwan Lolo lokacin da jirgin ta kife a cikin ruwa" inji shi.

Akalla 'yan kasuwa 53 ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a Kebbi
Hadarin jirgin ruwa

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Zagga ya ce daga cikin fasinjoji 100 da ke cikin jirgi, mutane 47 kawai aka ceto yayin da ba a iya ceto sauran ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu : An kashe Manjo Janar Ugbo da mutane bakwai a rikicin da ya barke a Benuwe

Shugaban ya ce hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tura masu ceto 500 don neman sauran mutanen.

A lokacin da yake bayani game da wannan lamarin, mukaddashin babban darakta na hukuman ba da agaji na gaggawa a jihar Kebbi, Alhaji Abbas Rabi'u, ya bayyana mummunan hadarin wani abin tausayi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng