Ko kun san nawa farashin Dala a yau?
- Farashin dala a kasuwar canji ya sauka zuwa Naira 367
- Samun dala a kasuwa ya fara wuya
- Babban bankin CBN ya saki dala a kasuwa
Farashin dala a kasuwar canji ya sauka zuwa Naira 367 a wasu wuraren kuma N366, yanzu haka samun dala a kasuwar canji ya dan yi wuya. A farkon sati kuwa canjin dala yana kamawa N365 zuwa N364 a kasuwa.
Babban banikin Najeriya a ranar Talata ya saki dala miliyan 259 a kasuwa.. Hakan ya sa canjin naira zuwa pound din kasar Ingila daga N476 ya koma zuwa N472 a canjin kudin Euro kuwa daga N436 zuwa N432 a ranar litinin.
A kasuwar duniya kuwa dalar Amurka daya ta kama a kan N359.43 daga N353.99 a ranar Litinin. A kudin pound din Ingila kuma ta kama N476.78 wanda a Litinin tana N467.08, a Euro kuma N425.24 daga N429.80 a ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Dafa alala a cikin leda yana janyo ciwon daji
Daga bakin Mista Isaac Okorafor kuwa darakta a bangaren sadarwa na CBN, ya shaida yadda CBN ta bi ka’ida domin samar da gaskiya a tsakanin ‘yan kasuwa. CBN na kara tabbatar da samar da darajar Naira a duniya a shaidawar da daraktan ya bayar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng