Dandalin Kannywood: An so in fito a yar madigo a wani fim din kudu amma naki amincewa - Rahma Sadau
Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la'akari da daga inda ta fito watau arewa.
Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la'akari da daga inda ta taso da kuma martaba al'ada da addinin yankin arewa.
KU KARANTA: Dole yan Najeriya su rungumi noma - Buhari
Legit.ng kuma dai ta samu cewa da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana'arta a dukkan fadin duniya.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.
Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon 'yar iska don kawai tana sana'ar ta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng