Bincike: Dafa alala a cikin leda yana kawo ciwon daji

Bincike: Dafa alala a cikin leda yana kawo ciwon daji

- Dafa abinci a cikin leda yana janyo ciwon daji

- Ledar in ta ji zafin wuta tana fitar da guba mai cutarwa

- Anfani da ganyen bishiya na gargajiya shine hanyar da bazata cutar ba

Ita dai alala abincin mutanen Najeriya ce wadda ake sarrafa ta daga wake, abinci ce a cikin dangin abinci masu gina jiki.

Wani mai bincike a kiwon lafiya, Mista John Tehinse ya gargadi mutane da su daina dafa abinci musamman alala a cikin leda don kuwa ledar na dauke da guba mai suna dioxins wanda yake janyo ciwon daji.

A wata gabatarwa da yayi ne a garin Ilorin a wata lakca da yayi ta 'Food Safety Control System in Nigeria' ya bayyana yadda dahuwar alala a leda ya yi yawa har da yawan mutane basu san hadarin da yake janyowa ba.

Bincike: Dafa alala a leda yana kawo ciwon daji
Bincike: Dafa alala a leda yana kawo ciwon daji

A yayin da ake dafa alala a cikin leda, ledar na fitar da wata guba ne idan ta ji zafin wuta, ita gubar mai suna dioxin tana yin lahani a cikin jikin dan adam har ta janyo ciwon daji.

A cikin lakcar shi ya yi kira da kungiyoyin kare lafiya ta Najeriya da masu sayar da abinci da su lura su daina yin hakan don lafiyar mutane.

Mista Tehinse ya bawa mutane shawara da su daina dafa alala a leda su fara anfani da ganyen bishiya, shine hanyar da bazata cutar da mutane ba.

DUBA WANNAN: Duba jerin sunayen tsoffin shugabannin jam'iyyar PDP

Hanya mafi lafiya yanzu da mutane suka gano shine dafa alalar a cikin ganye, wasu na anfani da ganyen bishiyar ayaba, wanda ma sia da ya kara sinadarin gina jiki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng