Wata yar Najeriya ta kafa tarihi a jami’ar Hertfordshire, ta kammala karatu da sakamako mafi kyawu (hotuna)
Wata matashiya yar Najeriya mai suna Folafoluwa Oginni ta kammala karatu a matsayin daliba mafi kwazo daga jami’ar Hertfordshire dake kasar Amurka.
An tattaro cewa matashiya Oginni ta kafa sabon tarihi bayan ta kammala karatu da sakamako mafi kyawu a fannin shari’a ba tare da ta taba samun karamin maki muddin rayuwarta a makarantar ba.
Oginni ta kuma kasance yar Najeriya ta farko da ta kammala a jamiár bayan ta kammala da rukunin 2017 a jami’ar Hertfordshire.
A shekara ta 2013, matashiyar ta kasance daliba mafi kokari a zaben kammala makarantar sakandare (WAEC) wanda aka rubuta a watannin Mayu/Juni na 2012.
KU KARANTA KUMA: Zahra Buhari ta yi shar da ita cikin sababbin hotuna
Bayan ta kammala makarantar sakandare, ta ci gaba a jami’ar Obafemi Awolowo inda zata karanci fannin shari’a amma dole ta bar makarantar bayan shekara daya saboda yajin aikin ASUU.
Daga baya Oginni ta kuma UK don ci gaba da karatunta na shari’a a jami’ar Hertfordshire.
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng